Hausa translation of the meaning Page No 310

Quran in Hausa Language - Page no 310 310

Suratul Maryam from 65 to 76


65. Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara a gare shi?
66. Kuma mutum yana cẽwa, « Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai? »
67. Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba?
68. To, Munã rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne.
69. Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya.
70. Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗanda suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita.
71. Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata. ( 1 ) Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce.
72. Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne.
73. Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, « Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa? »
74. Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ ( waɗandaMuka halakar ) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã. ( 2 )
75. Ka ce: « Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna! »
76. Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma.
( 1 ) Idan an tãra mutãne dõmin hisabi, anã ajiye wuta a tsakãnin mutãne da Aljanna, Sa'annan a gitta sirãɗi a cikan wutar dõmin mutãne su bia kansa su ƙẽtare wutar zuwa Aljanna kuma waɗansu su fãɗa a cikin wutar dõmin azãba dawwamamma kõ kuma ta ɗan lõkaci gwargwadon laifi.
( 2 ) Kãyan ɗãki na jin dãɗi kamar gadãje da kujẽri da kãyan cin abinci. Magãnã kuwa ita ce wurin da ake ganĩ ga mutum kamar tufãfinsa da sũrar jikinsa da dukan abingani daga gare shi.