Hausa translation of the meaning Page No 311

Quran in Hausa Language - Page no 311 311

Suratul Maryam from 77 to 95


77. Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: « Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya? »
78. Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?
79. Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa.
80. Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai.
81. Kuma suka riƙi gumãka, ( 1 ) baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.
82. Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.
83. Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu ( 2 ) a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?
84. Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar ajali ne kawai, ƙidãyãwa.
85. A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma.
86. Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa.
87. Ba su mal1akar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama.
88. Kuma suka ce: « Mai rahama Yã riƙi ã! »
89. Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni.
90. Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu.
91. Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama.
92. Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã.
93. Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã.
94. Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya.
95. Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar Ƙiyãma yanã shi kaɗai.
( 1 ) Gunki, shi ne dukan abin bautawa wanda bã Allah ba. Wanda ya riƙi wani sãlihi ko malã'iki ko aljani, yanã bauta masa, to, yã riƙe shi gunki ke nan. Bauta ita ce bin umurni da barin hani. Wanda ya bi umurnin da bã na Allah ba, kõ ya bar abin banin da ba na Allah ba, to, ya bauta wa mai umurnin ko mai hanin, yã riƙe shi gunki baicin Allah.
( 2 ) Idan shaiɗanu sun ga mai wa'azin gaskiya, sai su dinga shũshũta mabiyansu dõmin su yi faɗa da mai wa'azin, dõmin kada su saurare shi har su gãne ɓatarsu. Shaian shi ne mai ɓatar da wani, mutum ne kõ aljani.