Hausa translation of the meaning Page No 317

Quran in Hausa Language - Page no 317 317

Suratul Ta-Ha from 77 to 87


77. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, « Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa. »
78. Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su.
79. Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar ( dasu ) ba.
80. Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku.
81. Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi.
82. Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa.
83. « Kuma mẽne ne ya gaggautar ( 1 ) da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã! »
84. Ya ce: « Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda. »
85. Ya ce: « To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su. »
86. Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: « Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna? »
87. Suka ce: « Ba mu sãɓa wa alkawarinka ( 2 ) ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa. »
( 1 ) Mũsã ya zãɓi mutun sabã'in daga Banĩ Isrã'ĩla, dõmin su tafi wurin Mĩƙãti tãre, su ji maganar Ubangiji. A lõkacin da ya yi kusa, sai ya yi gaggãwadõmin bẽge. Kõ kuwa a bãyan azumin kwãna arba'in ya tafi a wurin Mĩƙãtin, Allah Ya fãra yi masa magana game da mutãnensa dõmin ɗẽbe masa kẽwa. Sai ya karɓa da cẽwa, « Sunã nan a kan sãwũna. » Wãtau sunã nan a kan abin da na ɗõra su a kansa na addini da aƙĩda ta tauhĩdi. Sai Allah Ya ce masa « A'aha! sun musanya addininkada bautar maraƙi. »
( 2 ) Alõkacin da Banĩ Isrã'ĩla zãsu fita daga Masar sun yi aron mundãyen mutãnen Masar dõmin su nũna cẽwa biki suke yi, bã gudu zã su yi ba, dõmin kada a bĩ su da wuri waɗannan mundãyen ne sãmiri ya tãra a bãyan tafiyar Mũsã zuwa ga Mĩƙãtin Ubangijinsa ya ƙẽra musu maraƙi mai jiki irin na mutãne da sauti irin na shãnu dõmin yã yi masa magudãnar iska a cikin cikinsa idan iskar ta fito, sai a jĩ ta da sauti kamar sautin kũkan shãnu. Kuma shi maraƙin bã ya dã wani rai, bã ya mõtsi, sai dai ƙũgin kawai.