Hausa translation of the meaning Page No 318

Quran in Hausa Language - Page no 318 318

Suratul Ta-Ha from 88 to 98


88. « Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta. »
89. Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni?
90. Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, « Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umurnĩna. »
91. Suka ce: « Ba zã mu gushe ba faufau a kansa munã mãsu lazimta, ( 1 ) sai Mũsã ya kõmo zuwa gare mu. »
92. ( Mũsã ) ya ce: « Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace. »
93. « Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne? »
94. ( Hãrũna ) ya ce: « Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba. »
95. ( Mũsã ) ya ce: « Mẽne ne babban al'amarinka? Ya Sãmiri! »
96. ( Sãmiri ) ya ce: « Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini. »
97. ( Mũsã ) ya ce: « To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi, ( 2 ) sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa. »
98. Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci ( 3 ) dukkan kõme da ilmi.
( 1 ) Lazimta a kan bauta wa maraƙin akwai wahala a cikinta dõmin haka aka kãwo wannan ƙissa sabõda a nũna cẽwa bautar Allah bãbu lazimta da wahala a cikinta duk abin da yake da wahala a cikinsa, bã addinin Allah ba ne. Akwai ĩ'itikãfi a cikin Musulunci wanda mafi yawansa kwãna gõma ne a cikin masallaci. Mutãnen Sãmiri ne suka fãra ibãda da kiɗa da rawa da wãƙã a cikin wurin ibãdarsu.
( 2 ) Mũsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya ƙõne maraƙin ya shẽke shi a cikin ruwan tẽku ya nũna ĩkon maraƙin ga kãre kansa daga wata cũta kuma da ƙarancinsa a cikin tẽku wadda take ɗaya ce daga cikin abũbuwan ĩkon Allah da suke iya gani, da lãlãcẽwar ibãdar mãsu bauta wa wanin Allah, a bãyan wahalarsu mai yawa ta lazimta a kansa.
( 3 ) Allah Ya yalwaci dukan kõme da sani, watau Yanã aikata kõme da ilminsa kuma Yanã umurni da bauta Masa da ilmi, wanda Ya aiki Manzanninsa da shi.