Hausa translation of the meaning Page No 32

Quran in Hausa Language - Page no 32 32

Suratul Al-Baqarah from 203 to 210


203. Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu. ( 1 ) To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku.
204. Kuma akwai daga mutãne ( 2 ) wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne.
205. Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa dõmin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shũka da 'ya'yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son ɓarna.
206. Kuma idan an ce masa: « Ka ji tsõron Allah, » sai girman kai da yin zunubi ya ɗauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma haƙĩƙa, shimfiɗa tã munana.
207. Kuma akwai daga mutãne ( 3 ) wanda yake sayar da ransa, dõmin nẽman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bãyi ne.
208. Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã ɗaya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan; lalle ne shĩ a gare ku maƙiyine, bayyananne.
209. To, idan kun karkace daga bayan hujjõji bayyanannu sun zo muku to ku sani cẽwa lalle ne Allah, Mabuwãyi ne, Mai hikima.
210. Shin suna jira, fãce dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwõyi na girgije, da malã'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su.
( 1 ) Bayãnin kabbarõri, bãyan sallõlin farillai gõma sha biyar, anã fãrawa da sallar azahar ta ranar salla a ƙãre da sallar asuba ta rãna ta huɗu daga rãnar salla. Kwãnukan Mina uku ne daga rãnar salla, saiga wanda ya yi gaggawa ya fita daga Mina bãyan fitar rãnar nan kuma gabãnin fãɗuwar rãna.
( 2 ) Bayãnin munafuki da hãlayensa, a cikin jama'a, a san shi, dõmin kada a dõgara a kansa. Haka mutumin kirki shi ma ana son a san shi dõmin a dogara da shi kamar yadda yayi bayãninsa.
( 3 ) Bayãnin mũmini sõsai a cikin Musulmi da halayensa, a sanshi dõmin a dõgara a kansa.