Hausa translation of the meaning Page No 33

Quran in Hausa Language - Page no 33 33

Suratul Al-Baqarah from 211 to 215


211. Ka tambayi Banĩ Isrã'ila, da yawa Muka bã su daga ãyõyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bãyan tã je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
212. An ƙawata rãyuwar dũniya ga waɗanda suka kãfirta, kuma suna izgili daga waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su, a Rãnar Ƙiyãma. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, bã da lissãfi ba.
213. Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin ( Littãfin ) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa. kuma bãbu wanda ya sãɓã, a cikinsa, fãce waɗanda aka bai wa shi daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu dõmin zãlunci a tsakãninsu. Sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi ĩmani ga abin da suka sãɓã a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya.
214. Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin waɗanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: « Yaushe taimakon Allah zai zo? » To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!
215. Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa ( 1 ) da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne.
( 1 ) Ciyar da mahaifa matalauta wãjibi ne haka ɗiya da 'ya'ya ƙanãna waɗanda bãsu da dũkiya har yãro ya balaga a kuma aurar da yãrinya ta tãre a gidan mijinta. Ammamãtar aure da bãwan mutum ciyar da su wãjibi ne kõ dã sunã da dũkiya. Liyãfa ga bãƙo har kwãna uku gwargwadon bukãta wãjibi ne, sauran ciyarwa mustahabbi ce bãyan an fitar da zakka idan tã wajaba.