Hausa translation of the meaning Page No 323

Quran in Hausa Language - Page no 323 323

Suratul Al-Anbiya from 11 to 24


11. Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta.
12. Sai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta.
13. « Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku. »
14. Suka ce: « Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci. »
15. Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu.
16. Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba.
17. Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun ( 1 ) riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa.
18. Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa.
19. Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurinSa ( watau malã'iku ) , bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya.
20. Sunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni.
21. Kõ ( kãfirai ) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa ( gare su ) ?
22. Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu ( sama da ƙasa ) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa.
23. Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su.
24. Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: « Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne. »
( 1 ) Abin wãsã, shi ne mãtã, kõɗã, kõ wani abin da ake shagaltuwa da shi.