Hausa translation of the meaning Page No 322

Quran in Hausa Language - Page no 322 322

Suratul Al-Anbiya from 1 to 10


Sũratul Anbiyã’
Tana karantar da dõkõkin Allah mãsu hukunta haɗuwar addinan Al1ah da haɗuwar aƙĩdõdinSu a kan kaɗaitar Allah Makaɗaici.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa.
2. Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa.
3. Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce ( sunã cẽwa ) « Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta? »
4. Ya ce: « Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani. »
5. Ã'a, suka ce: « Yãye- yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko. »
6. Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni?
7. Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato ( 1 ) idan kun kasance ba ku sani ba.
8. Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba.
9. Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa. ( 2 )
10. Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku, ( 3 ) a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta?
( 1 ) Ma'abũta ambato, watau mutãnen da aka bai wa littattafan sama: Yahũdu da Nasãra.
( 2 ) Mãsu yawaitãwa, sũ ne mãsu wuce haddõdin Allah ga Kõme, fãsiƙai da mãsu bidi'õ'i.
( 3 ) Al'ummar Muhammad, tsirar Allah da amincinsa su tabbata a gare shi. An saukar musu da Alƙur'ãni, a cikinsa akwai ɗaukakarsu da darajarsu, dõmin wanda aka ambata, to, an ɗaukaka shi.