Hausa translation of the meaning Page No 324

Quran in Hausa Language - Page no 324 324

Suratul Al-Anbiya from 25 to 35


25. Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa « Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini. »
26. Kuma suka ce: « Mai rahama ya riƙi ɗã. » Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, ( malã'iku ) bãyi ne mãsu daraja.
27. Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki.
28. Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõronSa.
29. Kuma wanda ya ce daga gare su, « Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa, » to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai.
30. Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke, ( 1 ) sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba?
31. Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu ( duwãtsun ) , tsammãninsu sunã shiryuwa.
32. Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirẽwa ne.
33. Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu ( 2 ) a cikin wani sarari suKe iyo.
34. Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama?
35. Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.
( 1 ) Abin wãsã, shi ne mãtã, kõɗã, Kõ wani abin da ake shagaltuwa da shi.
( 2 ) Wannan yã nũna cẽwa rãnã da watã a cikin sarari guda suke, Kõ da yake akwai nĩsan gaske a tsakãninsu.