Hausa translation of the meaning Page No 327

Quran in Hausa Language - Page no 327 327

Suratul Al-Anbiya from 58 to 72


58. Sai ya sanya su guntu- guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi.
59. Suka ce: « Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai. »
60. Suka ce: « Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm. »
61. Suka ce: « To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida. »
62. Suka ce: « Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm! »
63. Ya ce: « Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana. »
64. Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: « Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai. »
65. Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu ( sukace, ) « Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana. »
66. Ya ce: « Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah? »
67. « Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta? »
68. Suka ce: « Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa. »
69. Muka ce: « Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm. »
70. Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra.
71. Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai.
72. Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai.