Hausa translation of the meaning Page No 326

Quran in Hausa Language - Page no 326 326

Suratul Al-Anbiya from 45 to 57


45. Ka ce: « Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi, » kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi.
46. Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, « Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci. »
47. Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar Ƙiyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi.
48. Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa.
49. Waɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa'a.
50. Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi?
51. Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi.
52. Ya ce wa ubansa da mutanensa, « Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu? »
53. Suka ce: « Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu. »
54. Ya ce: « Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna. »
55. Suka ce: « Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãSu wãsã ne? »
56. Ya ce: « Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka. »
57. « Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya. »