Hausa translation of the meaning Page No 328

Quran in Hausa Language - Page no 328 328

Suratul Al-Anbiya from 73 to 81


73. Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu.
74. Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai.
75. Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai.
76. Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma.
77. Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
78. Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu.
79. Sai Muka fahimtar da ita ( mats'alar ) ( 1 ) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa.
80. Kuma Muka sanar da shi sana'ar ( 2 ) wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?
81. Kuma ( Muka hõre ) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme.
( 1 ) Asalin mats'alar, tumãkin wani mutum suka yi kĩwon ɓarna a gõnar wani a cikin dare alhãli kuwa anã kallafa wa mai dabbõbi ya kange dabbõbinsa da dare kamar yadda ake kallafa wa mai shũka da tsare shũkarsa a cikin yini. Sai Dãwũdu ya yi hukunci da cẽwa mai shũkar ya mallaki tumakin, shi kuma mai tumãki ya mallaki shũkar ɓãtacciya. Sai Sulaimãn ya gyãra hukuncin da cẽwa mai gõna ya riƙi tumãkin ya rãyu a kansu har a lõkacin da mai dabbõbin ya gyãra masa gonarsa har ta Koma yadda take a farKon lõkacin,sa'an nan ya mayar da tumãkin ya karɓi gõnarsa. A cikin ƙissar akwai nũnin cẽwa Annabãwa bã su saunar faɗin gaskiya, sabõda wani mutum duk yadda yake, kuma anã warware hukunci idan kuskure ya auku a ciki, kuma Annabãwa sunã yin kuskure ga abin da bai shãfi wahayiba. Kuma kõmãwa ga askiya idan tã bayyana wajibi ne.
( 2 ) Wannan yanã nũna wajabcin yin sana'a wadda mutum ke rãyuwa a kanta. Kuma yanã nũna wajabcin aiki da sabubba dõmin nẽman tsaron kai. Bã ya halatta ga mutum ya yi kwance bãbu sanã'ar da zai tsayu a kanta Kõ kuma ya gĩtta kansa ga halaka da tãwilin tawakkali. Tawakkali shĩ ne mayar da ãƙibar al'amura ga Allah a bãyan mutum ya yi abinda yake iya yi.