Hausa translation of the meaning Page No 34

Quran in Hausa Language - Page no 34 34

Suratul Al-Baqarah from 216 to 219


216. An wajabta ( 1 ) yãƙi a kanku, alhãli kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba.
217. Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: « Yin yãƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah. » Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma waɗannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.
218. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fãtar ( sãmun ) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
219. Suna tambayar ka game da giya da cãcã. ( 2 ) Ka ce: « A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu. » Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: « Abin da ya rage. » ( 3 ) Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni.
( 1 ) Bayãnin hukuncin yãƙi da wuri da lõkacin da aka hana yinsa, da dalilin yinsa.
( 2 ) Bayãnin hukuncin cãca da giya da ciyarwa ta alhẽri. Cãca da giya harãmun ne dõmin cũtarsu tã fi amfaninsu yawa, ana huknnci da abin da ya rinjãya. Ayõyin wata sura sun bayyana haramcin.
( 3 ) Abin da ya rage daga larũrarku da ta iyãlanku da wanda ciyar da shi yake wãjibi a kanku, saura shi ne afwu. Daga afwu ake sadakar taɗawwu'i.