Hausa translation of the meaning Page No 335

Quran in Hausa Language - Page no 335 335

Suratul Al-Hajj from 24 to 30


24. Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga, hanyar wanda ake gode wa.
25. Lalle ne waɗanda suka kãfirta kuma suka taushe ( mutãne ) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutãne alhãli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar ( 1 ) da gaskiya a cikinsa da zãlunci zã Mu ɗanɗana masa daga wata azãba mai raɗadi.
26. Kuma a lõkacin da Muka iyãkance ( 2 ) wa Ibrãhim wurin Ɗakin ( Muka ce masa ) , « Kada ka haɗa kõme da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake ƊãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu tsayuwa da mãsu ruku'u da mãsu sujada. »
27. « Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi. »
28. « Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci. »
29. « Sa'an nan kuma sai su ƙãre ibãdarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawãfi ( sunã gẽwaya ) ga Ɗãkin nin 'yantacce. »
30. Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce- hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbõbin ni'ima ( 3 ) fãce abin da ake karantãwa a kanku. Sabõda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumãka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur.
( 1 ) Ilhãdi, shĩ ne yin ibãda bã yadda Allah Ya yi umurni da a yi ta ba. Wanda ya yi nufin karkatar da gaskiyar ibãda a cikin hurumin Makka, Allah zai yi masa azãba mai tsanani,balle fa a ce mutum ya aikata. Sabõda haka yanã wajaba ga mai nufin zuwa Hajji ya kõyi yadda ake yin ibãda kãfinya tafi Makka dõmin kada ya jãwo wa kansa halaka.
( 2 ) Allah Ya nũna wa Ibrahĩm iyãkar Ɗãkin Ka'aba da iska, sa'an nan ya fãra ginashi, kumaYa nuna masa iyãkõkin Hurumin Makka, ya sanya alãmõmi.
( 3 ) Dabbõbin ni'ima, sũ ne raƙumai da shãnu da tumãki da awãki. An halatta cinsu sai waɗanda suka mutu a gabãnin a yanka. Kuma shaidar zur kamar bauta wa gumãka take wajen sabbaba azãba, dõmin anã halattar da haram kõ aharamtar da halat game da ita.