Hausa translation of the meaning Page No 336

Quran in Hausa Language - Page no 336 336

Suratul Al-Hajj from 31 to 38


31. Kuna mãsu tsayuwa ga gaskiya dõmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yanã kamar abin da ya fãɗo daga sama, sa'an nan tsuntsãye su cafe shi, ko iska ta fãɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa.
32. Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita ( girmamãwar ) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda.
33. Kuna da waɗansu abũbuwan amfãni ( 1 ) a cikinta ( dabbar hadaya ) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattãta zuwa ga Ɗãkin 'yantacce ne.
34. Kuma ga kõwace al'umma Mun sanya ibãdar yanka, dõmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbõbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushãra ga mãsu ƙanƙantar da kai.
35. Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukãtansu su firgita, da mãsu haƙuri a kan abin da ya sãme su, da mãsu tsayar da salla, kuma sunã ciyarwa daga abin da Muka azurta su. ( 2 )
36. Kuma rãƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibãdõjin Allah. Kunã da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sunã tsaye ( 3 ) a kan ƙafãfu uku. Sa'an nan idan sãsanninsu suka fãɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hõre muku su, tsammãninku kunã gõdẽwa.
37. Nãmõminsu bã za su sãmi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tanã, sãmun Sa. Kamar haka Ya hõre su sabõda ku dõmin ku girmama Allah sabõda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushãra ga mãsu kyautata yi.
38. Lalle ne, Allah Yanã yin faɗa ( 4 ) sabõda waɗanda suka yi ĩmãni. Lalle ne Allah bã Ya son dukkan mayaudari, mai yawan kãfirci.
( 1 ) Anã amfãni da dabbar hadaya wajen hawa sabõda larũra da shan nõno har a kai ga wurin sõke ta. Anã sõke hadaya a cikin hurumin Makka.
( 2 ) Waɗannan sũ ne siffõfin mãsu ƙasƙantar da kai wataumãsu tawãli'u. Zukãtansa na firgita idan an ambaci Allah, su ga kamar sunã ganin sa, a gaba gare su, sabõda haka sai su ji sauƙin haƙuri ga ɗaukar masifa, kuma su tsayar da salla da sauran ibãdõdi na jiki kuma su bãyar da zakka da sauran ibãdõdin dũkiya.
( 3 ) Wannan yanã nũna yadda ake sũkar rãƙuma sunã tsaye a kan ƙafãfu uku a ɗaure guda bãyan an lanƙwasa guiwarta an ɗaure sama. Anã ambatar sũnan Allah kuma a yi kabbara a lõkacin sũkar a masõkar zũciyarta. Anã sukar shãnu kuma anã yankansu. Anã yankan tumãki da awaki kawai. Anã yanka sauran dabbõbi da tsuntsaye kawai.
( 4 ) Allah Yã yi alkawarin kãre wanda yake aiki da taƙawa dõminsa. Yanã tunkuɗe masa maƙiyansa, Ya yi masa faɗa.