Hausa translation of the meaning Page No 337

Quran in Hausa Language - Page no 337 337

Suratul Al-Hajj from 39 to 46


39. An yi izni ga waɗanda ake yãƙar su da cẽwa lalle an zãlunce su, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa,Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu.
40. Waɗanda aka fitina daga gidajensu bã da wani hakki ba fãce sunã cẽwa, Ubangijinmu Allah ne. « Kuma ba dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne ba, sãshensu da sãshe, haƙĩƙa, da an rũsa sauma'õ'in ( Ruhbãnãwa ) dã majãmi'õ'in Nasãra da gidãjen ibãdar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yanã taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne haƙĩƙa Mai ƙarfi Mabuwãyi. »
41. Waɗanda suke idan Muka bã su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani, ( 1 ) kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma ãƙibar al'amura ga Allah take.
42. Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙĩƙa, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa, sun ƙaryata a gabaninsu.
43. Da mutãnen Ibrahim da mutãnen Lũɗu.
44. Da mãsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsã. Sai Na jinkirtawa kãfiran, sa'an nan kuma Na kãma su. To, yãya musũNa ( gare su ) ya kasance?
45. Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhãli kuwa tanã mai zalũnci sai ta zama fãɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wõfintar, da kuma gidãjen sarauta maɗaukaka.
46. Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dõmin zukãta waɗanda zã su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurãre da su su kasance a gare su? Dõmin lalle ne idãnun ba su makanta, amma zukãta waɗanda ke a cikin ƙirãza sũ ke makanta.
( 1 ) Abin da aka sani daga shar'ia watau shĩ ne alhẽri, kuma abin da ba a sani ba ga shari'a, watau sharri wanda Allah bã Ya so, akasin alhẽri. Tsayar da ayyukan alhẽri ba zai isa ba sai anã yin wa'azi ga mutãne a umarce su da yin alhẽri kuma a hana su daga aikata sharri.