Hausa translation of the meaning Page No 338

Quran in Hausa Language - Page no 338 338

Suratul Al-Hajj from 47 to 55


47. Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini ( 1 ) ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa.
48. Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azãba gare ta ( da laifinta ) sa'an nan Na kãma ta, kuma zuwa gare Ni makõma take.
49. Ka ce: « Ya ku mutãne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa. »
50. To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sunã da gãfara da arziki na karimci.
51. Kuma waɗanda suka yi aikin ɓãtãwa a cikin ayõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahĩm ne.
52. Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri, ( 2 ) sai Shaiɗan ya jẽfa ( wani abu ) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyinSa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
53. Dõmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfãwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukãtansu akwai cũta, da mãsu ƙẽƙasassun zukãtansu. Kuma lalle ne azzãlumai haƙĩƙa, sunã a cikin sãɓãnimai nĩsa.
54. Kuma dõmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka dõmin su yi ĩmãni da shi sabõda zukãtansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmãni ne zuwa ga hanya madaidaiciya.
55. Kuma waɗanda suka kãfirta bã zã su gushe ba sunã a cikin shakka daga gare shi, har Sa'a ta jẽ musu bisa ga abke, kõ kuwa azãbar wani yini bakarãre ta jẽ musu.
( 1 ) Allah bã Ya sãɓa wa'adinSa.Daɗẽwar rashin saukar azãba bã sãɓãwar wa'adi ba ne, ajalin azãbar ne bai zo ba.Dõmin yini guda a wurin Allah daidai yake da shẽkara dubu na shẽkarun dũniya. Sabõda haka kwana guda daidai yake da shẽkara dubu biyu. Sabõda haka sa'a guda ta Allahna daidai da shẽkara tamãnin da uku da wata huɗu.
( 2 ) Annabãwa sukan yi wahami ga tunãninsu, su yi zaton wani abu daidai ne alhãli kuwa a wurin Allah bã haka Yake nufi ba. A kan wannan, sai shakka ta shiga wãwã a kansu, amma wanda ke da ĩmãni to bã zai rikice ba sabõda wannan kuskure dõmin Allah bã Ya barin su a kansa, sai Ya gyãra abin da ke ciki na wahami. Misãli ƙissar Yũnusu, da ƙissar Annabi a cikin suratu Abasa, da ƙissar Ibrãhim wajen jãyayya da malã'ikun da aka aika zuwa alƙaryõyin mutãnen Lũɗu.