Hausa translation of the meaning Page No 343

Quran in Hausa Language - Page no 343 343

Suratul Al-Mu'minun from 18 to 27


18. Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne.
19. Sai Muka ƙãga muku, game da shi ( ruwan ) , gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci.
20. Da wata itãciya, ( 1 ) tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ.
21. Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni ( 2 ) mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ
22. Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku.
23. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: « Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba? »
24. Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: « Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji ( kõme ) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko. »
25. « Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci. »
26. Ya ce: « Ya Ubangijĩna! Ka taimakeni sabõda sun ƙaryatani. »
27. Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. « Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni ( sabõda wani ) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne. »
( 1 ) Itãciyar Zaitũni. Ita ce itãciyar farko da ta tsira a kan ƙasa a bãyan Ɗũfãna tanã rãyuwa mai dõgon lõkaci; an ce tanã rãyuwa kamar shẽkara dubũ huɗu. Anã cin 'ya'yanta, anã man shãfãwa da su, kuma anã yin miya dasu. Asalin sibg, rini dõmin tanã rina lõmar tuwo. Dũtsen Sĩnã'a mai albarka, ɗũr, shĩ ne dũtSe mai itãce a kansa.
( 2 ) Sũfi da gashi dõmin tufãfi da kãyan ɗãki, kãsũsuwa da fãtu da kõfatai dõmin yin abũbuwan amfãni.