Hausa translation of the meaning Page No 344

Quran in Hausa Language - Page no 344 344

Suratul Al-Mu'minun from 28 to 42


28. « Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: » Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai. « »
29. « Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.' »
30. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu jarrabãwa.
31. Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu.
32. Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. « Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba? »
33. Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: « Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã. »
34. « Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne. »
35. « Shin, yanã yi muku wa'adin ( cẽwa ) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne? »
36. « Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi. »
37. « Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa, ( 1 ) kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba. »
38. « Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba. »
39. Ya ce: « Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni. »
40. Ya ce: « Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma. »
41. Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai!
42. Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu.
( 1 ) Munã mutuwa kuma munã rãyuwa da haihuwar ɗiya da 'yã'ya. A bãyan wannan bãbu wata rãyuwa ta wata Lãhira,