Hausa translation of the meaning Page No 346

Quran in Hausa Language - Page no 346 346

Suratul Al-Mu'minun from 60 to 74


60. Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu,
61. Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su ( ayyukan alhẽri ) .
62. Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su.
63. Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan ( magana ) , kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su,mãsu aikatãwa ne.
64. Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa.
65. Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku.
66. Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya.
67. Kunã mãsu girman kai gare shi ( Annabi ) , da hĩrã kunã alfãsha.
68. Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar ( Alƙur'ãni ) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu?
69. Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi?
70. Kõ sunã cẽwa, « Akwai hauka gare shi? » Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne.
71. Kuma dã gaskiya ( Alƙur'ãni ) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton ( 1 ) ( darajar ) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa.
72. Kõ kanã tambayar su wani harãji ne ( a kan iyar da Manzanci a gare su ) ? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa.
73. Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya.
74. Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne.
( 1 ) Zikiri a nan, shi ne Alƙur'ãni wanda ya zo wa Lãrabãwa kõ Ƙuraishawa da abũbuwa na ɗaukakarsu, da ambatonsũnansu, da shiryar da su, da gabãtar da su a kan sauran kabĩlu. Amma duk da haka sunã bijirẽwa daga gare Shi.