Hausa translation of the meaning Page No 347

Quran in Hausa Language - Page no 347 347

Suratul Al-Mu'minun from 75 to 89


75. Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa.
76. Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba ( 1 ) sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u.
77. Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi. ( 2 )
78. Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.
79. Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku.
80. Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba?
81. Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa.
82. Suka ce: « Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lal1e ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne? »
83. « Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko. »
84. Ka ce: « Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani? »
85. Zã su ce: « Ta Allah ne. » Ka ce, « Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba? »
86. Ka ce: « Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma? »
87. Zã su ce: « Na Allah ne. » Ka ce, « Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba? »
88. Ka ce: « Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani? »
89. Zã su ce: « Ga Allah yake. » Ka ce: « To, yãya ake sihirce ku? »
( 1 ) Azãbar dũniya kamar yunwa da ciwo da talauci da rashin kwanciyar hankali.
( 2 ) Mugi, shi ne kãsa yin magana sabõda ɗẽbe tsammãni daga sãmun kõwane alhẽri. Asalin kalmar daga Fulãtanci take.