Hausa translation of the meaning Page No 345

Quran in Hausa Language - Page no 345 345

Suratul Al-Mu'minun from 43 to 59


43. Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
44. Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne ( waɗanda ) bã su yin ĩmãni!
45. Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli bayyananne.
46. Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya.
47. Sai suka ce: « Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne. »
48. Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku.
49. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu ( 1 ) zã su shiryu.
50. Kuma Mun sanya Ɗan Maryama, shi da uwarsa wata ãyã ( 2 ) Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.
51. Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi ( 3 ) kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
52. Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa. ( 4 )
53. Sai ( al'ummar ) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu- guntu, ( 5 ) kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.
54. To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci.
55. Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya,
56. Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri?
57. Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu,
58. Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni,
59. Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki,
( 1 ) Banĩ Isrã'ĩla na yanzu idan sun tuna cẽwa Alƙur'ãni bã shĩ ne farkon littafin sama ba, an bai wa Mũsã wani littafi, su kuma sunã alfahari da shi.
( 2 ) Ãyar Ĩsã da uwarsa ita ce an haife shi bãbu uba. Kuma a lõkacin nan Yahũdu suka so sarkin zãmanin nan ya kashe shi, sai uwarsa ta gudu da shi zuwa Baitil Maƙaddas, kõ Dimashƙa, kõ Falasɗĩnu, inda suka zauna shẽkara gõma sha biyar har sarkin nan ya mutu.
( 3 ) Allah Ya umurci ManzanninSa da cin halat sa'an nan su aikata aikin ƙwarai. Haka kuma Ya umurci Mũminai. Sabõda haka karɓar aiki na ƙwarai an tsayar da shi ne a kan cin halat.
( 4 ) Taƙawa, ita ce bauta wa Allah da abin da Ya yi umurni a bauta Masa, a kan harshenAnnabinsa na zamaninsa. Yanzu bãbu taƙawa sai a cikin Musulunci kawai.
( 5 ) Kõwa ya kãma hanyarsa, al'ummar Musulmi ta zama ƙungiyõyi dabam- dabam, kõwanensu yanã farin ciki da abin da ke gare shi, yanã ganin shi ne mafifici.