Hausa translation of the meaning Page No 349

Quran in Hausa Language - Page no 349 349

Suratul Al-Mu'minun from 105 to 118


105. « Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa? »
106. Suka ce: « Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu. »
107. « Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci. »
108. Ya ce: « Ku tafi ( da wulãkanci ) a cikinta. Kada ku yi Mini magana. »
109. Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, « Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi. »
110. Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya.
111. Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
112. Ya ce: « Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru? »
113. Suka ce: « Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa. »
114. Ya ce: « Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani. »
115. « Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba? »
116. Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja.
117. Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ ( kiran ) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara.
118. Kuma ka ce: « Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama. »