Hausa translation of the meaning Page No 348

Quran in Hausa Language - Page no 348 348

Suratul Al-Mu'minun from 90 to 104


90. Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
91. Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne ( akwai abin bautawa tare da Shi ) , lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa.
92. Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
93. Ka ce: « Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi. »
94. « Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai. »
95. Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi.
96. Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ neMafi sani game da abin da suke siffantãwa.
97. Ka ce: « Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge- fizgen Shaiɗãnu. »
98. « Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni, ( 1 ) »
99. Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: « Yã Ubangijina, Ku mayar da ni ( dũniya ) . »
100. « Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari. » Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su.
101. Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba.
102. To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
103. Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama.
104. Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne.
( 1 ) Inã nẽman tsari da Kai, yã Ubangijina! Kada Shaiɗãnu su halarto ni a cikin al'amurana duka, dõmin ba su halarta, fãce da sharri.