Hausa translation of the meaning Page No 351

Quran in Hausa Language - Page no 351 351

Suratul Al-Nur from 11 to 20


11. Lalle ne waɗanda ( 1 ) suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma.
12. Don me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce: « Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne? »
13. Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata.
14. Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne,dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa.
15. A lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a wurin Allah, babba ne.
16. Kuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, « Bã ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma » ?
17. Allah Yanã yi muku wa'azi, kada ku kõma ga irinsa, har abada, idan kun kasance mũminai.
18. Kuma Allah Yanã bayyana muku ãyõyinSa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
19. Lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ ba ku sani ba.
20. Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa. Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai!
( 1 ) Farko Hadĩsil Ifk ne wanda waɗansu suka jẽfi Ã'isha, Ummul Mũminĩna da zina a cikinsa Allah Ya barrantar da ita. Bai zama sharri ba ga Musulmi, sai dai ya zama alhẽri dõmin ya zama sanadi ga sanin hukunce- hukunce mãsu yawa, na zaman jama'a da kuma darajar mutãnen da abin ya shãfa. Yadda ƙissar take shi ne yadda Ã'ishatu, Uwar Mũminai ta faɗa, ta ce: « Na kasance tãre da Annabi tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cikin wani yãƙi, a bãyan an saukar da Hijãbi, watau kulle. Sai ya ƙãre daga yãƙin ya kõma, ya yi kusa da Madĩna, sai ya yi umurni da tãshi ga tafiya a wani dare, sai ni kuma na tafi na ƙãre sha'anĩna, na fuskanta zuwa ga wurin rãƙumãta, sai na ga abin wuyana ya yanke, saina kõma, na neme shi, kuma su mãsu kula da ni suka ɗauki darbũka suka aza a kan rãkuma sunã zaton inã ciki alhãli mãtã sun kasance sauƙãƙa dõmin ba su cin kõme sai kaɗan na abinci. » Na sãmi abin wuyãna na kõmo a bãyan sun tafi. Sai na zaunaa masaukĩna wanda na kasance a ciki. Kuma na yi zaton mutãnen zã su rasa ni su kõmo zuwa gare ni. Sai na ji barci na yi barcin. Shi kuma Safwãnu ya yi rurumi daga bãyan ãyarin yãƙi, ya fita da sauran dare sai ya wãyi gari a inda nake. Sai ya ga duhun mutum mai barci, sai ya gãne ni a lõkacin da ya gan ni, dãmã ya kasance yanã ganĩ na a gabãnin kulle, sai na farka da jin sautinsa na istirjã'i. « A lõkacin da ya gãne ni, sai na rufe fuskãta da mayãfina. Wallãhi bai yi mini magana ba da kalma, ni kuma ban ji kõ kalma ba daga gare shi, sai dai istirjã'insa a lõkacin da ya gurfanar da rãƙumarsa, ya take ƙafarta ta gaba, ni kuma nã hau, ya shiga yanã jan rãƙumar da ni har muka isa ga uwar yãƙin, a bãyan sun sauka, a cikin zãfin rãna. Daga nan wanda ya halaka ya halaka, wanda ya jiɓinci girman abin, shi ne Abdullahi bn Ubayyi bn salũl. » Buhãri da Muslimu sun ruwaito shi.