Hausa translation of the meaning Page No 356

Quran in Hausa Language - Page no 356 356

Suratul Al-Nur from 44 to 53


44. Allah Yanã jũyar da dare da yini. Lalle ne a cikin wannan akwai abin kula ga ma'abũta gannai.
45. Kuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafãfu biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yãna halitta abin da Yake so, lalle Allah, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne.
46. Lalle ne haƙĩƙa Mun saukar da ãyõyi, mãsu bayyanãwa. Kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya.
47. Kuma sunã cẽwa, « Mun yi ĩmãni da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗã'ã. » Sa'an nan kuma wata ƙungiya daga gare su,su jũya daga bãyan wancan. Kuma waɗancan ba mũminai ba ne.
48. Kuma idan aka kirã su zuwa ga Allah da ManzonSa, dõmin Ya yi hukunci ( 1 ) a tsakãninsu, sai gã wata ƙnngiya daga gare su sunã mãsu bijirewa.
49. Kuma idan hakki ya kasance a gare su, zã su jẽ zuwa gare shi, snnã mãsu mĩƙa wuya.
50. Shin, a cikin zukãtansu akwai cũta ne, ko kuwa sunã tsõron Allah Ya yi zãlunci a kansu da ManzonSa? Ã'a, waɗancan sũ ne azzãlumai.
51. Maganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu takan kasance kawai su ce « Mun ji, kuma mun yi ɗã'ã, Kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara. »
52. Kuma wanda ya yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsõron Allah, ya kuma bĩ Shi da taƙawa to waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
53. Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙĩƙa sunã fita.' Ka ce, « Kada ku rantse, ɗã'ã sananna ce! Lalle ne, Allah Mai ƙididdigewã ne ga abin da kuke aikatãwã. »
( 1 ) Wannan yanã nũna cẽwa rashin yardã da hukuncin Allah kãfirci ne. Wanda ya kai ƙãra ga kõtun al'ada alhãli kuwa yanã Musulmi kuma ya halatta haka, bã da wata lalũra ba, ya zama kãfiri sai idan ya tũba. Bã ya halatta ga Musulmi su yarda da yin kõtunanal'ãda a ƙasarsu.