Hausa translation of the meaning Page No 357

Quran in Hausa Language - Page no 357 357

Suratul Al-Nur from 54 to 58


54. Ka ce: « Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu. Kuma bãbu abin da yake a kan Manzo fãce iyarwa bayyananna. »
55. Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai.
56. Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo, tsammãninku a yi muku rahama.
57. Kada lalle ka yi zaton waɗanda suka kãfirta zã su buwãya a cikin ƙasa, kuma makõmarsu wuta ce, kuma lalle ne makomar tã mũnana.
58. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni ( 1 ) sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
( 1 ) Ladabin shiga gida shĩ ne dukan yãron da ya balaga, ɗa ne kõ bãwa, kada ya shiga gida kõ a ɗãki a bãyan sallama sai ya nẽmi izni da cẽwa « In shiga? » Idan an karɓa masa da izni, ya shiga, idan kuma yanã zaton ba a ji shi ba, sai ya sãke nẽman izni har sau uku. Nẽman izni yanã wajaba kõ ga yãran gidan a cikin lõkuta uku, wãtau a gabãnin sallar asuba da lõkacin tsakar rãnar na ƙailũla da bãyan sallar ishã'i.