Surah An-Nur | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 358
Suratul Al-Nur from 59 to 61
59. Kuma idan yãra daga cikinku suka isa mafarki to su nẽmi izni, kamar yadda waɗanda suke a gabãninsu suka nẽmi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
60. Kuma tsõfaffi daga mãtã, waɗanda bã su fatan wani aure to, bãbu laifi a kansu su ajiye tufãfinsu, bã sunã mãsu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shĩ ne mafi alhẽri a gare su. Kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
61. Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci ( abinci ) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku, ( 1 ) gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali.
( 1 ) Akwai daga ladubban zamantakẽwa har dai a tsakãnin dangi a ci abincin jũna, kõ aci tãre a waje guda, kõ kuwa kõwa ya ci dabam. Kuma idan an haɗu a yi gaisuwã a tsakãnin jũna, gaisuwa irin wadda Allah Ya ce Musulmi su yi wa jũnansu da cẽwa « Assalãmu alaikum » . Ita ce gaisuwa mai kyau. Anã ƙãra « Wa rahmatul Lãhi wa barakãtuh, » dõmin ta ƙãra dãɗi.