Hausa translation of the meaning Page No 359

Quran in Hausa Language - Page no 359 359

Suratul Al-Nur from 62 to 2


62. Waɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai ( 1 ) .
63. Kada ku sanya kiran Manzo ( 2 ) a tsakãninku kamar kiran sãshenku ga sãshe. Lalle ne Allah Yanã sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗãɗe. To, waɗanda suke sãɓãwa daga umurninSa, su yi saunar wata fitina ta sãme su, kõ kuwa wata azãba mai raɗãɗi ta sãme su.
64. To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa, Yanã sanin abin da kuke a kansa kuma a rãnar da ake mayar da su zuwa gare shi, sai Yanã bã su lãbãri game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kõme, Masani ne.
Sũratul Furkãn
Tanã karantar da yin kira ga tauhĩdi da kõre shubhõhi daga Alƙur’ani Mai girma, da kuma Annabi tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da ( Littãfi ) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta.
2. wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa.
( 1 ) Babban ladabin haɗuwar jama'a shĩ ne ĩmãni da Allah kuma da ManzonSa. Sa'an nan kuma biyayya ga shũgaba wajen ayyukan gayya na rãyuwa haɗe, kamar ginin masallaci da hanya da kãsuwa da maƙabarta. Shũgaba yanã da ĩkon bãyar da iznin fakuwar mai uzuri, kuma yanã da ĩkon hanãwa gwargwadon hãli. Wannan kuma ya nũna muhimmancin aikin gayya da tsayuwar shũgaba a kansa, da wajabcin karɓa kira zuwa gare shi. Kuma wannan yanã nũna halaccin karɓar harãji daga mutãne dõmin a tsayu da bukãtocin haɗuwar jama'a gwargwadon hãli.
( 2 ) Wannan yanã nũna ladabin yadda ake kiran Manzon Allah tã hanya mai ladabi. Kada a kira shi da sũnansa kamar yadda ake kiran sauran mutãne da 'Yã Ali', 'Ya zaid,' sai dai a ce Yã Manzon Allah! a cikin sauti mai laushi mai dãɗi. Kuma wannan ladabi yanã shãfar dukan Musulmi na kõwane zãmani game da shũabansu wanda yake shũgabantar su ga al'amurransu na zamantakẽwa. Kuma wannan yanã nũna rashin kyãwon mãsu cewa sunã zikiri da kiran sũnan Allah kamar haka « Allah! Allah! Allah! » Sabõda rashin ladabin da ke cikin yin haka ga Manzon Allah balle ga Allah.Ba a yin addini sai yadda Allah Yake son a yi Masa, wãtau yadda AnnabinSa ya shiryar da mutãne dõmin su bi Shi, su yi aiki da shi, Kuma sãɓã wa umurnin Annabi yanã sabbaba fitina ga mutãne kõ kuma ga ƙasa gabã ɗaya.