Hausa translation of the meaning Page No 364

Quran in Hausa Language - Page no 364 364

Suratul Al-Furqan from 44 to 55


44. Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida ( 1 ) suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.
45. Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta.
46. Sa'an nan Muka karɓe ta ( inuwa ) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi.
47. Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi ( kamar Tashin Ƙiyãma ) .
48. Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamarSa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama.
49. Dõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta.
50. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa ( 2 ) shi ( Alƙur'ãni ) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci.
51. Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi ( 3 ) a ciƙin kõwace alƙarya.
52. Sabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma.
53. Kuma shĩ ne Ya garwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurɓatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa.
54. Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi.
55. Kuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su, kuma kãfiri ya kasance mai taimakon ( Shaiɗan ) a kan Ubangijinsa.
( 1 ) Dabbõbin gida sun fi rashin hankali bisa ga na dãji, dõmin na dãji na gudun abin da zai cũce sũ su kuma dabbõbin gida sunã zumã tãre da mãsu cin su, su shã nõnonsu kuma su kashe 'ya'yansu.
( 2 ) Sarrafa Alƙur'ãni watau Munsanya shi a cikin misãlai dabam- dabam dõmin su gani kõ su ji, su yi tunãni, amma sai suka ƙi saurãren, sai dai kãfirci.
( 3 ) Dã Muna so dã Mun aika wa kõwane gari da Annabinsa mai yi musu gargaɗi, amma ba Mu so haka ba, sai Muka aika ka kai ɗaya zuwa ga dukan dũniya dõmin Mu ɗaukaka darajarka.