Hausa translation of the meaning Page No 365

Quran in Hausa Language - Page no 365 365

Suratul Al-Furqan from 56 to 67


56. Ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi.
57. Ka ce: « Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya ( 1 ) zuwa ga Ubangijinsa. »
58. Kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa.
59. Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da ( 2 ) Shi.
60. Idan aka ce musu, « Ku yi sujada ga Mai rahama. » Sai su ce: « Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu? » Kuma wannan ( magana ( 3 ) ta ƙãra musu gudu.
61. Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai ( 4 ) ( na tafiyar wata ) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta.
62. Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa,ga wanda yake son ya yi tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde.
63. Kuma bãyin Mai rahama ( 5 ) su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: « Salãma » ( a zama lafiya ) .
64. Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu.
65. Kuma waɗanda suke cẽwa « Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra ( 6 ) »
66. « Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni. »
67. Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma ( ciyarwarsu ) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa.
( 1 ) Bã na nẽman wata ijãra sabõda inã karanta muku Alƙur'ãni, ko, sabõda inã shiryar da ku, amma wanda ya so ya ciyar da dũkiyarsa dõmin Allah, to, shĩ kam bã ni hana shi, sai ya ciyar. Kuma mun sani Annabi ba ya cin sadaka. A kan haka ne waɗansu Malamai suka hana karɓar ijãraa kan karantar da Alƙur'ãni. Abin da yake Mu'utamadi ya halatta sabõda Hadĩsi, kumada sauƙaƙẽwa ga aikin yãɗa addĩnin Musulunci. Hukumci yanã canzawa da canzãwar hãli.
( 2 ) Idan kanã son sanin siffofinAllah, sai ka tambayi Allah, dõmin bãbu wanda ya san shi, sani na gani balle ya iya gaya maka yadda Yake, sabõdahaka siffõfin Allah da sũnãyenSa duka bã a yin shisshigi a gare su, sai yadda aka ji su daga Manzon Allah.Tauƙifiyyai ne.
( 3 ) Kõ sun san gaskiyar abin daaka kira su zuwa gare shi, bã zã su yi ɗã'ã ba, dõmin wai sunã jin nauyi su karɓi umurni daga wani mutum.
( 4 ) Taurãri bakwai waɗandaake cẽ wa matafa su ne Mirrikh da Zahra da Uɗãrid da Ƙamar, wãtau Watã, da Rãnã, da Mushtari, da Zuhal; Kuma burjõji sũ gõma sha biyu ne, su ne Himlu, da Saur, da Zaujã'a, da Sirtãn, da Asad, da Sunbula da Mĩzãn da Aƙrab, da Ƙausu, da Jadyu,da Dalwu da Hũt.
( 5 ) Bãyan da ya ambaci masu ƙin su yi sujada ga Mai rahama sabõda kangararsu sai kumaya fãra ambaton siffofin mãsu son yin sujada gare shi, Yãyi musu sunã Bãyin Mai rahama.
( 6 ) Garama, ita ce uƙũba da dũkiya mai lazimtar wanda aka aza wa ita. Da Hausa anã cẽwa tãra. Watau azãba da zã tafi ƙarfin jiki har tanã nẽman wani abu wanda ya danganci jiki. Kõ mẽne ne, kamar dũkiya.