Hausa translation of the meaning Page No 363

Quran in Hausa Language - Page no 363 363

Suratul Al-Furqan from 33 to 43


33. Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara.
34. Waɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya.
35. Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna, mataimaki tãre da shi.
36. Sai Muka ce: « Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yinMu. » sai Muka darkãke su, darkãkewa.
37. Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai.
38. Da Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan, mãsu yawa.
39. Kuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da ( shi ) , halakarwa.
40. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, ( Ƙuraishi ) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa ( a Ƙiyãma ) .
41. Kuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, ( sunã cẽwa ) « Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo? »
42. « Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba. » Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya!
43. Shin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa?