Hausa translation of the meaning Page No 366

Quran in Hausa Language - Page no 366 366

Suratul Al-Furqan from 68 to 77


68. Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,
69. A riɓanya masa azãba a Rãnar Ƙiyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce.
70. Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai.
71. Kuma wanda ya tũba, ( 1 ) kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah.
72. Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci.
73. Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah,bã su saukar da kai, sunã kurame ( 2 ) da makãfi.
74. Kuma waɗanda suke cẽwa « Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya ( 3 ) mu shũgabanni ga mãsu taƙawa. »
75. Waɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci.
76. Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni.
77. Ka ce: « Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku ( 4 ) ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci. »
( 1 ) Wanda ya tũba daga kõwane irin zunubi, waɗanda aka ambata da waɗanda ba a ambata ba, kõ dã laifinsakãfirci ne, to, sai ya tũba zuwa ga Allah kawai, tũba ta gaskiya, lalle ne Allah zai karɓi tũbarsa matuƙar ajalin mutuwa bai sauka a kansa ba.
( 2 ) Idan an yi musu wa'azi zã su saurãre shi, kuma su yi aiki da shi. Bã zã su zama kurãme ba ga karɓar gaskiya, kuma bã zã su zama makãfi ba gaganin hanyar shiryawa.
( 3 ) Anã son mutum ya rõƙi Allah Ya ɗaukaka shi, shi da zuriyarsa, ɗaukakar addini, kamar yadda Annabi Ibrãhĩm ya yi rõƙon haka. Kuma wannan yanã cikin sifõfin Bãyin Mai rahama.
( 4 ) Wannan yanã nũna cẽwa Allah Yanã son bãyinSa mãsu rõƙonsa. Kuma Yanã son a rõkeShi ƙwarai.