Hausa translation of the meaning Page No 367

Quran in Hausa Language - Page no 367 367

Suratul Al-Shu'ara from 1 to 19


Sũratush Shu‘arã’
Tanã karantar da cẽwa addinin Allah abu guda ne kuma shi ne gaskiyã. Manzannin Allah kõ da yake sun yi maganã da harsuna dabam- dabam a cikin lõkutta mãsu nĩsan gaske, amma duk da haka ba su sãɓã wa jũna ga ma’anõnin abin da suka faɗa ba. Sauran addinai duka ƙarya ne, masu sãɓã wa jũna.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ɗ. S̃. M̃.
2. Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
3. Tsammãninka kai mai halakar ( 1 ) da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!
4. Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
5. Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
6. To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.
7. Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?
8. Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
9. Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
10. Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, « Ka je wa mutãnen nan azzãlumai. »
11. « Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba? »
12. Ya ce: « Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni. »
13. « Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci ( 2 ) kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna. »
14. « Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni. »
15. Ya ce: « Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre. »
16. « Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne. »
17. « Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu. »
18. Ya ce: « Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka? »
19. « Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai? »
( 1 ) Wannan yã nũna cẽwa Annabi Muhammadu yanã jin tsõron rashin ĩmãnin mutãnensa, kada ya zama shĩ ne ya gajarta daga abin da Allah Ya ɗõra a kansa, na iyar da manzanci. Haka mũmini yake, kullum girman Ubangijinsa yake dũbi, sabõda haka kõme ya yi na ɗã'a, sai ya ga kãsãwar kansa ga tsayuwa da hakkin Ubangijinsa, a kansa, ya ƙãra jin tsõro da tawãli'u.
( 2 ) Mũsa yanã nũna cẽwa, shi yanã jin tsõro kada ya zama ya gajarta wajen iyar da manzanci, dõmin shi mai saurin fushine, yanã nẽman a taimake shi ɗan'uwansa Hãrũna.Wannan ya yi kama da farkon sũrar inda Annabi, tshĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya nũna tsõron taƙaitãwa ga iyar da manzancin Allah zuwa ga mutãnensa dõmin haka ba su yi ĩmãni ba. Hãlin Annabawa duka ɗaya ne ga tsõron taƙaita aikin Ubangijinsu.