Hausa translation of the meaning Page No 370

Quran in Hausa Language - Page no 370 370

Suratul Al-Shu'ara from 61 to 83


61. Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: « Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne. »
62. Ya ce: « Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni. »
63. Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa « Ka dõki tẽku da sandarka. » Sai tẽku ta tsãge, ( 1 ) kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.
64. Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.
65. Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.
66. Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.
67. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
68. Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.
69. Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.
70. A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, « Mẽne ne kuke bauta wa? »
71. Suka ce: « Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su. »
72. Ya ce: « Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira? »
73. « Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku? »
74. Suka ce: « Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa. »
75. Ya ce: « Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa? »
76. « Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa? »
77. « To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu. »
78. « Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni. »
79. « Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni. »
80. « Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni. »
81. « Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni. »
82. « Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako. »
83. « Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai. »
( 1 ) Tẽku ta tsãge hanya gõma sha biyu a kan adadin danginBanĩ Isrãĩla. Suka bi suka wuce, sa'ilin nan aka nutsar daFir'auna, shi da jama'arsa, a cikin hanyõyin ruwan,