Hausa translation of the meaning Page No 371

Quran in Hausa Language - Page no 371 371

Suratul Al-Shu'ara from 84 to 111


84. « Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya ( 1 ) a cikin mutãnen ƙarshe. »
85. « Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima. »
86. « Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu. »
87. « Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su. »
88. « A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi. »
89. « Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki. »
90. Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.
91. Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.
92. Kuma aka ce musu, « Inã abin da kuka kasance kunã bautawa? »
93. « Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu? »
94. Sai aka kikkife su ( 2 ) a cikinta, su da halakakkun.
95. Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.
96. Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,
97. « Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna. »
98. « A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu. »
99. « Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi. »
100. « Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta. »
101. « Kuma bã mu da abõki, masõyi. »
102. « Sabõda haka dã lalle munã da ( dãmar ) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai! »
103. Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.
104. Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
105. Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.
106. A lõkacin da ɗan'uwansu, Nũhu, ya ce musu, « Shin, bã zã ku yi taƙawa ba? »
107. « Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce. »
108. « To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. »
109. « Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu. »
110. « Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. »
111. Suka ce: « Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka? »
( 1 ) Harshen gaskiya shĩ ne yabõ mai kyau. Mutãnen ƙarshe sũ ne Musulmi al'ummar Annabi Muhammadu, mãsu shaida ga annabawa da iyar da manzanci.
( 2 ) Gumãkan, sũ da halakakku mabiyansu. Dukkan mai ɓatarda wani shĩ ne gunki ga maibin sa halakakke.