Hausa translation of the meaning Page No 369

Quran in Hausa Language - Page no 369 369

Suratul Al-Shu'ara from 40 to 60


40. « Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya. »
41. To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna, « Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya? »
42. Ya ce: « Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai. »
43. Mũsã ya ce musu, « Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa. »
44. Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: « Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya. »
45. Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.
46. Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.
47. Suka ce: « Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta. »
48. « Ubangijin Mũsa da Hãrũna. »
49. Ya ce: « Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa,zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya. »
50. Suka ce: « Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu. »
51. « Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni. »
52. Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ( 1 ) ne.
53. Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.
54. « Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan. »
55. « Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne. »
56. « Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne. »
57. Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.
58. Da taskõki da mazauni mai kyau.
59. Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.
60. Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.
( 1 ) Fir'auna da mayãƙansa zã su bĩku dõmin su kãma ku. Ammãbã zã su sãmi ĩkon kãma kuba.