Hausa translation of the meaning Page No 373

Quran in Hausa Language - Page no 373 373

Suratul Al-Shu'ara from 137 to 159


137. « Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen ( 1 ) mutãnen farko. »
138. « Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba. »
139. Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ.Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
140. Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
141. Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni.
142. A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: « Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba? »
143. « Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce. »
144. « Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. »
145. « Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu. »
146. « Shin, anã barin ku ( 2 ) a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu? »
147. « A cikin gõnaki da marẽmari. »
148. « Da shuke- shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi ( 3 ) mãsu narkẽwa a ciki? »
149. « Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari? »
150. « Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. »
151. « Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata. »
152. « Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa. »
153. Suka ce: « Kai daga mãsu sihiri kurum kake. »
154. « Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya. »
155. Ya ce: « Wannan rãkuma ce tanã da shan ( 4 ) yini, kuma kunã da shan yini sasanne. »
156. « Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku. »
157. Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma.
158. Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
159. Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai.
( 1 ) Wãtau lãbarun mutãne waɗanda ba su ci gaba ba bã su son a yi rawa da nishãɗi. Anã karantawar ma'anar ƙaryar ta farko, watau wai tãtsũniya ce: a ce wai a hana ãyã akan tsaunuka dõmin wasanni. Suna nufi da ãya ko alãma gidãjen rawa da na nashãdi watau stadiyam da kasĩno.
( 2 ) Kuna zaton zã a bar ku a irin wannan ni'ima' Allah bã zai karɓi rãyukanku ba kuma Ya yi muku hisãbi a kanta? Kayya! Zã a yi muku hisãbi a bãyan kun mutu an tsayar da ku, dõmin hisãbin ayyukan da kuka yi.
( 3 ) Hirtsi shi ne 'ya'yan itãce sãbabbi tun ba su nuna ba. Wãtau hirtsin gonakinsu idan an ci shi narkẽwã ya ke yi a cikin ciki, balle kuma 'ya'yan itãce nunannu.
( 4 ) Kuna zaton zã a bar ku a irin wannan ni'ima' Allah bã zai karɓi rãyukanku ba kuma Ya yi muku hisãbi a kanta? Kayya! Zã a yi muku hisãbi a bãyan kun mutu an tsayar da ku, dõmin hisãbin ayyukan da kuka yi.