Hausa translation of the meaning Page No 372

Quran in Hausa Language - Page no 372 372

Suratul Al-Shu'ara from 112 to 136


112. Ya ce: « Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa. »
113. « Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa. »
114. « Ban zama mai kõre mũminai ba. »
115. « Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa. »
116. Suka ce: « Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, ( daga maganarka, ) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa »
117. Ya ce: « Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni. »
118. « Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai. »
119. Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.
120. Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.
121. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
122. Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.
123. Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni.
124. A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, « Bã zã ku yi taƙawa ba? »
125. « Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce. »
126. « Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. »
127. « Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu. »
128. « Shin, kunã yin ginin sitadiyo ( 1 ) a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa? »
129. « Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama? » ( 2 )
130. « Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa. »
131. « To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. »
132. « Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani. »
133. « Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya. »
134. « Da gõnaki da marẽmari. »
135. « Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma. »
136. Suka ce: « Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba. »
( 1 ) Sitãdiyo shi ne gidan wasanni da Turanci, alãmã da Lãrabci.
( 2 ) Kõ kuma wurãren sanã'õ'i kamar masãƙoƙi irin na zãmanin nan.