Hausa translation of the meaning Page No 383

Quran in Hausa Language - Page no 383 383

Suratul Al-Naml from 64 to 76


64. Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita,kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: « Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya. »
65. Ka ce: « Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su. »
66. Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne.
67. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: « Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne? »
68. « Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko. »
69. Ka ce: « Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take? »
70. Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci.
71. Kuma sunã cẽwa, « A yaushe wannan wa'adi ( zai auku ) , idan kun kasance mãsu gaskiya? »
72. Ka ce: « Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta ( 1 ) a gare ku. »
73. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kanmutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa.
74. Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa.
75. Kuma bãbu wata ( mas'ala ) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne.
76. Lalle ne wannan Alƙur'ãni ( 2 ) yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.
( 1 ) Kuturi, shi ne a bãyan wani ya hau dabba ya kuma aza wani a kanta daga bãya gare shi. Kinaya ce na cẽwa abin yanã kusa gare su ƙwarai, kamar tsakãnin ɗan kuturi da mahayin dabba.
( 2 ) Idan wannan Alƙur'ani ya ƙunsã ilmin asĩrai da yake iya gaya wa Banĩ Israĩla mafi yawan abin da sũ da kansu, suke sãɓã wa jũna a kansu, tãre da shahararsu da ilmi, da yawan Annabãwan da suka wuce a cikinsu, to, ga Lãrabãwa jãhilai hiyãka ke nan. Bãbu abin da ya wajaba a gare su, sai sallamawa ga abin da yake kiran zuwa gare shi. In abin da yake faɗa ba gaskiya ba ne, dã Banĩ Isrãĩla ne farkonmãsu nũna ƙaryarsa. Ammã ba su yi ba. Sabõda haka duka gaskiya ne. Sai kõwa ya bĩ shi ya tsĩra.