Hausa translation of the meaning Page No 382

Quran in Hausa Language - Page no 382 382

Suratul Al-Naml from 56 to 63


56. Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce « Ku fitar da mutãnen Lũɗu daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki. »
57. Sai Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa, ( 1 ) fãce mãtarsa, Mun ƙaddara ta a cikin mãsu wanzuwa.
58. Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa. To, ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.
59. Ka ce: « Godiya ta tabbata ga A1lah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa. » Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi? ( 2 )
60. Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa ( Allah da wani ) .
61. Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba.
62. Kõ wãne ne yake karɓã , kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni.
63. Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku,kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi.
( 1 ) Mutãnensa mũminai. Ĩmãni da gaskiya idan gaskiya ta bayyana asĩri ne daga asĩran Allah sai wanda Ya bai wa. Kusanci ga wani Annabi da aure kõ zumunta, bã ya bãyar da shi. Ruwan azãba, shĩ ma asĩri ne na Allah.
( 2 ) Daga wannan ãyã ta 59 zuwa ƙarshen Sũra, duka tambĩhi ne ga abũbuwan fake na ilmin Allah, wanda ya shãfi jikunanmu, amma ba mu san yadda suke aukuwa a gare mu ba. Sa'an nan kuma da tambĩhi ga abũbuwan gaibi da suke zuwa dõmin mu yi ĩmãni da su.