Hausa translation of the meaning Page No 384

Quran in Hausa Language - Page no 384 384

Suratul Al-Naml from 77 to 88


77. Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai.
78. « Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani. »
79. Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya.
80. Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya.
81. Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa ( al'amari zuwa ga Allah ) .
82. Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba ( 1 ) daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa « Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni. »
83. Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. ( ga kõra )
84. Har idan sun zo, ( Allah ) zai ce, « Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa? »
85. Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta cẽwa.
86. Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.
87. Kuma da rãnar ( 2 ) da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu.
88. Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa.
( 1 ) Wata dabba ce anã kiranta Jassãsa an ce 'yar rãƙumar Sãlihu ce a lõkacin da aka kashe uwarta, ta gudu, ta shiga cikin dũtse' dũtsen ya rufe da ita. Tanã fitõwa daga dũtsen Safa a Makka da hantsi. Bãyan fitõwarta, bãbu sauran wa'azi. Mũmini ya tabbata mũmini kãfiri kuma ya tabbata haka. Tanã riƙe da sandar Mũsã da Hãtimin Sulaimãn. Tana fitõwa a bãyan fitõwar rãnã daga yamma. Allah ɗai Ya san gaskiyar yadda take.
( 2 ) Bãyan fitõwar dabba, kuma sai bũsar ƙahõ na farkõ, sa'an nan na biyu sa'an nan Ƙiyãma.