Hausa translation of the meaning Page No 385

Quran in Hausa Language - Page no 385 385

Suratul Al-Naml from 89 to 5


89. Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita, ( 1 ) a yinin nan, amintattu ne.
90. Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa?
91. ( Ka ce ) : « An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, ( 2 ) Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa. »
92. « Kuma inã karanta Alƙur'ãni. » To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: « Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake. »
93. Kuma ka ce: « Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu. » Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.
Sũratul Ƙasasi
Tanã karantar da nũna falalar hijira dõmin addini kuma tanã kwaɗaitarwa ga yin hijira.Kada tsõron barin.Dũkiya, da ɗiya Su kange mũmini daga yin hijira da addininsa zuwa ga wurin yardar Allah wanda Yake Shi ne Mai kõme kuma Yanã riƙe da kõme Shi kaɗai.Kuma tana hanã rarraba jama’ar Musulmi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ɗ. S̃. M̃.
2. Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
3. Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
4. Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya- ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.
5. Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.
( 1 ) Firgita daga azãbar Lãhira, wannan firgita ba irin ta farko ba ce wadda aka ambata a cikin ãyã ta 87, dõmin wancan firgitar kwarjini ce a bãyan tãshi daga kaburbura.
( 2 ) Wannan Gari shĩ ne Makka. Sanya Makka hurumi ba a iya shiga cikinsa da yãki yanã a cikin ashĩrai na Allah. Shiryuwa da ɓata duka asĩrai ne na Allah. Tsãrin Alƙur'ani da abubuwan da ya ƙunsa duka asĩran Allah ne.