Hausa translation of the meaning Page No 394

Quran in Hausa Language - Page no 394 394

Suratul Al-Qasas from 71 to 77


71. Ka ce: « Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar Ƙiyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji? »
72. Ka ce: « Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar Ƙiyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani? »
73. « Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde. »
74. Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: « Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa » ( 1 )
75. Kuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: « Ku kãwo dalilinku. » Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu.
76. Lalle ne Ƙãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita ( 2 ) daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a ( 3 ) ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, « Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa. »
77. « Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa, ( 4 ) lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna. »
( 1 ) Bãyan Allah Ya tunãtar da Musulmi rahamarSa da kaɗaita ga bãyar da ni'ima kõ hana ta da siffõfi mãsu kwaɗaitar da mũmini ga ɗã'a ga Allah da ManzonSa, daga cikin ɗã'ã akwai yin hijira wanda yake shĩ ne kan lãbãrin sũrar, sai kuma Ya tsõratar da mai bin wanin Allah ga rashin yin hijira. Duka abin da ya hana mũminai hijira idan shi abin nan ba uzuri ne na shari'a ba, to, ya zama gunki, abin bautãwa, wanin Allah. Umurnin da ya sãɓa wa umurnin Allah duka, umurnin abõkin tãrayya ne ga Allah ga wanda ya bĩ shi.
( 2 ) Asalin baghy zãlunci, amma ga izɗilãhi, shi ne fita daga ɗã'ar shugaban Musulmi.
( 3 ) Yawan su saba'in, an ce arba'in, kuma an ce gõma.
( 4 ) Ɓarna a cikin ƙasa, shi ne fita daga tsarin jama'a, da rabasu ƙungiya- ƙungita, ko barin hijira a bãyan an yi umurni da yin ta.