Hausa translation of the meaning Page No 393

Quran in Hausa Language - Page no 393 393

Suratul Al-Qasas from 60 to 70


60. Kuma abin da aka bã su daga kõme, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shĩ ne mafi alhẽri, knma mafi wanzuwa. Shin bã ku hankalta?
61. Shin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa'an nan shi a Rãnar Ƙiyãma yanã daga mãsu shiga wuta?
62. Kuma rãnar da ( Allah ) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: « Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa? »
63. Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: « Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba. »
64. Kuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa ( 1 ) !
65. Kuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: « Mẽne nekuka karɓa wa Mananni? »
66. Sai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnaosu ba.
67. To, amma wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni' ya aikata aiki na ƙwarai, to, akwai fãtan su kasance daga mãsu cin nasara.
68. Kuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba.Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma ( Allah ) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
69. Kuma Ubangijinka Yanã sanin abin da zukãtansu ke ɓõyẽwa, da abin da suke bayyanãwa.
70. Kuma Shĩ ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kuma Shi ne abin gõdiya a cikin ta farko ( dũniya ) , da ta ƙarshe ( Lãhira ) . Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
( 1 ) An shãfe jawãbi. ƘaddarawarSa ita ce: « Dã Sun kaSance sunã shiryuwa a dũniya, dã ba su gan ta ba a Lãhira. »