Surah Al-Qasas | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 395
Suratul Al-Qasas from 78 to 84
78. Ya ce: « An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai. » Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba? ( 1 )
79. Sai ( Ƙãrũna ) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: « Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa Ƙãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne. »
80. Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: « Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, ( 2 ) kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai ha ƙuri. »
81. Sai Muka shãfe ƙasa ( 3 ) da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.
82. Kuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, « Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara. »
83. Wancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take.
84. Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
( 1 ) Yanã ganin dũkiyar da ya samu, ya sãme ta ne sabõda ya san ilmin fatauci da sana'a kuma yanã da ƙarfin nẽman dũkiyar, sabõda raddin irin tunãninsa Allah Ya ce Ya halaka wanda ya fi shi tsananin ƙarfi da ƙõƙarin tãra dũkiya, kuma idan Ya tãshi halaka mai laifi bã Ya tsayãwa tambayarsa dalĩlin da ya sa ya yi laifin kãfin Ya halakar da shi. Waɗannan abũbuwa uku sun isa ga mai dũkiya ya yi tunãni, dõmin kada annashuwa ta shige shi ya ƙi gõde waAllah.
( 2 ) ĩmãni da aikin ƙwarai wanda Allah Ya yi umurui da a yi shi, kuma yinsa kamar yadda ManzonSa ya nũna. Akwai daga cikin aikin ƙwarai yin hijira da barin kula da dũkiya. Bã a sãmun sakamakon Allah sai da haƙuri.
( 3 ) An ce a bãyan Ƙãrũna ya yanke kansa da nasa mutãne daga Mũsã, sai ya shirya da wata kãruwa dõmin ta yi wa Mũsã ƙazafin cẽwa ya yi zina da ita, a kan ya aure ta. Sai Mũsãya tãshi yanã wa'azi a cikin Banĩ Isrã'ĩla ya ce: « Yã Banĩ Isrã'ĩla wanda ya yi sãta zã mu yanke hannunsa, wanda yayi ƙazafi mu yi masa bũlãla tamãnin, wanda ya yi zina, bã ya da mãtã, mu yi masa bũlãla ɗãri, wanda ya yi zina yanã da mãtã, mu jẽfe Shi sai yã mutu. » Sai Ƙãruna ya ce: « Kõ dã kai ne? » Ya ce: « Kõ da ni ne. » Sai Kãrũna ya ce: « An ce kã yi fãjirci tãre da wance, kãruwa. » Sai Mũsã ya ce: « A kirã ta » Da ta zo, ya gama ta da Allah, ta faɗi gaskiya, sai ta ce Ƙãrũna ne ya yi tsãda da ita, ta faɗi hakanan. Sai Mũsã ya yi addu'a a kansa, ƙasa ta haɗiye shi, shi da gidansa duka.