Surah Al-Baqarah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 40
Suratul Al-Baqarah from 246 to 248
246. Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta ( 1 ) daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: « Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah. » Ya ce: « Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba? » Suka ce: « Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu? » To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.
247. Kuma annabinsu ( 2 ) ya ce musu: « Lalle ne, Allah ya naɗa muku Ɗãlũta ( 3 ) ya zama sarki. » Suka ce: « Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya? » Ya ce: « Lalle ne, Allah Yã zãɓe shi a kanku, kuma Ya ƙãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani. »
248. Kuma annabinsu ya ce musu: « Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin ( 4 ) nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku ( ta naɗin Ɗãlũta daga Allah ne ) idan kun kasance mãsu ĩmãni. »
( 1 ) Wannan ƙissa tana nũna cẽwaba a iya yin yãƙi sai da sarki' shũgaba. Kuma ta fai dalĩlinda ke sanya jama'a su yi yãƙi; watau dõmin tsaron addinida rãyuka da nasaba da mutunci da dũkiya.
( 2 ) Sũnan Annabinsu Shamwĩlu daga Sibt Lãwaya A bãyan Mũsã Yũsha'u bin Nũn sa'an nan Kãlib, sa'an nan Hizƙĩl, sa'an nan Ilyas sa'an nan Alyasa'u, daga nan Bani Isrã'ila suka rasa mai jan su har Amãliƙa ɗiyan Amlĩƙ bn Ãd waɗanda ke zaune a Falastĩn suka rinjãyi Bani Isrã'ila, suka karkashe su suka kõre sudaga gidãjensu suka kãma 'ya'yansu, har a lõkacin da wata mace daga Sibt Lãwaya ta haifi Shamwĩlu Annabi. Ya naɗa musu sarki Ɗãlũta.
( 3 ) Ɗãlũta yana a cikin gidan Binyãminu ɗan Ya'aƙũbu talakãwa ne sunã dõgara a kansanã'a. Zũriyyar Yahũza, sũ nesarãkuna dõmin haka sunansu ya rinjãya a kan Bani Isra'ila. Zũriyyar Lãwaya sũ ne Annabãwa da mãlamai.
( 4 ) Akwatin Natsuwa, an saukar da shi tãre da Ãdam a cikinsa akwai sũrõrin annabãwa, da gãdon riƙonsa ya kai ga Mũsã yanã sanya Attaura a ciki sabõda haka aka sãmi karyayyun allunan Attaura a ciki da rawanin Harũna da wani abu daga Mannu da Salwa. A lõkacin da Amãliƙa suka rinjãye su,sai suka karɓe wannan akwãti suka ajiye shi inda bai dãceda shi ba, har a lõkacin da malã'iku suka ɗauke shi zuwa ga Ɗãlũta.