Hausa translation of the meaning Page No 39

Quran in Hausa Language - Page no 39 39

Suratul Al-Baqarah from 238 to 245


238. Ku tsare ( 1 ) lõkatai a kan sallõli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai ga Allah.
239. To, idan kun ji tsõro, to ( ku dai yi salla gwargwadon hali ) da tafiya ƙasa kõ kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya nũna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba.
240. Kuma waɗanda suke mutuwa ( 2 ) daga gare ku, alhãli suna barin mãtan aure, wasiyya ga mãtan aurensu da dãɗaɗãwa zuwa ga shekara guda bãbu fitarwa, to, idan sun fita to bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.
241. Kuma waɗanda aka saki suna da dãɗaɗãwa gwargwadon hãli, wajabce a kan mãsu taƙawa ( 3 ) .
242. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa; tsammãninku, kuna hankalta.
243. Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita ( 4 ) daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: « Ku mutu. » Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa.
244. Kuma ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mai jĩ ne, Masani.
245. Wãne ne wanda ( 5 ) zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku.
( 1 ) Bayãnin hukuncin tsare lõkutan salla a cikin kõwane hãli: aminci ko tsõro, da bãyar da salla yadda hãli ya bãyar duka; tsaye kõ da tafiya kõ gudãne. Hikimar sanya wannan hukunci a tsakãnin hukunce- hukuncen aure dõmin farkarwa a kan muhimmancin salla, dõmin kada mu'ãmala ta shagaltar da Musulmi daga gare ta.
( 2 ) Al'ãda idan ba ta sãɓã wa rukunin sharĩ'a ba bã a hana ta sai dai bãbu tilastãwa ga yinta. A zamanin Jãhiliyya mãtã suna iddar mutuwar mazansu shẽkara guda. Wanda ya yi wasiyyar kada matarsa ta fita daga ɗãkinta har shẽkaraana karɓar masa sai dai bãbu tĩlas a gare ta da ta zauna, dõmin an shãfe hukuncin iddar shẽkara ta al'ãdar Jãhiliyya.
( 3 ) Bayãnin hukuncin dãɗaɗãwa ga mãtan da aka saki bãyan an yi zaman aure da su Tamattu'i gare su wãjibi ne a kan mazansu, gwargwadon hãli.
( 4 ) Wasu mutãne ne daga cikin Bani Isrã'ila annõba tã auku a kansu sai suka fita daga gidãjensu dõmin gudun mutuwa sũdubũ huɗu kõ takwas kõ wanin wannan adadi, sai Allah Ya ce musu; « Ku mutu, » sai suka mutu kwana takwas kõ fiye da haka. Sa'an nan kuma Allah Ya tãyar da su dõmin Ya nũna musu cẽwa gudun mutuwa, bã ya hana ta, sai abin da Ya so, shi ke aukuwa. Wannan ƙissa tanã amfãnar da ƙarfafa rãyuka dõmin jihãdi, sabõda haka umurni da yãƙi ya bĩ ta; watau ita shimfiɗa ce ga umurnin jihãdida fita zuwa yãƙi. Kuma sũrarna karantar da tattalin arziki daga nan zuwa ƙarshenta. Watau kafa gari wajibi ne ga tattalin arziki.
( 5 ) Bãyãni ga cẽwa jihãdi bã ya yiwuwa sai mutãne kõwa yabãyar da taimakonsa na dũkiya kõ na ma'ana. Kuma duk wanda ya bãyar da taimako, to, rance ne ya bai wa Allah, Wanda yake Shi ne Ya bãyar da asalin dũkiyar, da yawa kõkaɗan, kuma Mai sakamako ga wanda ya yi aiki da umurninSa da babban sakamako, bãyan an kõma zuwa gareShi. Jihãdi wãjibi ne ga tattalin arziki domin tsaro.