Surah Al-Baqarah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 41
Suratul Al-Baqarah from 249 to 252
249. A lõkacin da Ɗãlũta ya fita ( 1 ) da rundunõnin, ya ce: « Lalle ne Allah Mai jarrabarku ne da wani kõgi. To, wanda ya sha daga gare shi, to, ba shi daga gare ni, kuma wanda bai ɗanɗane shi ba to lalle ne shi, yana daga gare ni, fãce, wanda ya kamfata, kamfata guda da hannunsa. » Sai suka sha daga gare shi, fãce kaɗan daga gare su. To, a lõkacin da ( Ɗãlũta ) ya ƙẽtare shi, shi da waɗanda suka yi ĩmani tãre da shi, ( sai waɗanda suka sha ) suka ce: « Babu ĩko a gare mu yau game da Jãlũta da rundunõninsa. » Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle sũ mãsu gamuwa ne da Allah, suka ce: « Da yawa ƙungiya kaɗan ta rinjayi wata ƙungiya mai yawa da iznin Allah, kuma Allah Yana tãre da mãsu haƙuri. »
250. Kuma a lõkacin da suka ( 2 ) bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: « Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai. »
251. Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dãwudu ya kashe Jãlũta, kuma Allah Ya bã shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma bã dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne sãshensu da sãshe ba lalle ne dã ƙasa tã ɓãci; kuma amma Allah Ma'abũcin falala ne a kan tãlikai.
252. Waɗancan ayõyin Allah ne: Muna karanta su a kanka da gaskiya: Kuma lalle ne kai, hakĩka, kana daga manzanni.
( 1 ) Sõja na bukãtar tarbiya, su sãbã da wahala da ƙishirwa da magana mai shiryarwa. Kõgin kuwa shĩ ne kõgin Urdun tsakãnin Urdun da Falastĩn.
( 2 ) Dãwũdu ɗan Ãisha ya gãji annabcin Shamwĩlu da mulkin Ɗãlũta, shĩ ne ya fãra haɗã su a cikin Bani lsrã'ila bãyansa sai ɗansa Sulaimãn ya gãje shi haka nan. Yawan mutãnen Ɗãlũta da suka yi yãƙi kamar adadin mutãnenBadar ne waɗanda suka yi yãƙi tãre da Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.