Hausa translation of the meaning Page No 406

Quran in Hausa Language - Page no 406 406

Suratul Al-Rum from 16 to 24


16. Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba.
17. Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya. ( 1 )
18. Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli.
19. Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku.
20. Kuma akwai daga ãyõyinSa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa.
21. Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. ( 2 ) Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.
22. Kuma akwai daga ãyõyinSa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi.
23. Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa.
24. Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.
( 1 ) Akwai dangantaka a tsakãnin tasbĩhi, watau ibãda da rãyuwa, da tsakãnin fitar hantsi da sãfiya kamar yadda yake akwai dangantaka a tsakãnin mutuwa da maraice, da yamma da kãfirci
( 2 ) Akwai dangantaka a tsakãnin halittar namiji da mace daga yumɓu da kuma natsuwar dasuke sãmu daga junã da sõyayya da rahamar da ke a ciki.